Pages

Sunday 8 December 2019

Kwankwaso ya jinjinawa Ahmed Musa da Adam A. Zango bisa daukar nauyin karatun dalibai

Tsohon gwamnan Kano Sanat Rabiu Musa Kwankwaso ya jinjinawa tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa kasar Saudiyya kwallo, Ahmed Musa da tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango bisa daukar nauyin karatun matasa da suka yi.



A kwanakin bayane, Adam A. Zango ya bayyana daukar nauyin karatun wasu matasa sama da 100 a garin Zaria inda jama'a da dama suka jinjina masa hakanan shima Ahmed Musa bayan da ya zama jakadan jami'ar Sky Line dake Kano ya bayyana cewa zai dauki nauyin karatun dalibai a makarantar.

Kwankwaso a wata hira da yayi da Kwankwasiyya TV dake shafin Instagram wanda kuma ta wallafa wani sashe na hirar a shafinta, ya bayyana cewa abinda Ahmed Musa yayi abune me kyau dan duk wanda yayi karatu a jami'ar da Sky line kamar yayine a hadikwatar jami'ar dake Dubai.

Hakanan ya jinjinawa Adam A. Zango inda ya bayyana cewa, wannan abune me kyau kuma ba sai lallai mutum da yawa za'a dauki nauyin karatunsu ba koda guda daya mutum zai iya yayi dan kuwa baisan Alherin da zai jawowa kansa da 'yan uwansa ba da wanda ya dauki nauyin karattun.

Kwankwaso dai yayi suna wajan daukar nauyin karatun dalibai, musamman 'ya'yan talakawa, a satin daya gabata, ina cikin jirgi na ji wasu da suka yi karatu a Masar ke labarain cewa akwai lokacin da suna masar din suka je tarbar wasu daga ciki  daliban da Kwankwaso ya aika karatu can, suka ce da ka kansu kaga 'ya'yan talakawa, dan wasunsu ma watakila ko cikin Kano basu taba zuwa ba.


Ji bayanin Kwankwason a kasa:






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment