Pages

Saturday 7 December 2019

Mahaifin Hasat Idris ya rasu

Inna lillahi wa inna iaihi Raji'un, Allah ya yiwa mahaifin tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris Rasuwa. Hafsat ce da kanta ta saka wanan hoto a shafinta na sada zumunta inda ta sanar da rasuwar mahaifin nata sannan ta yi rokon da a sakashi a addu'a.



Abokan sana'ar ta da dama da suka hada da Rukayya Dawayya, Teema Makamashi, Aminu Abba Umar, Nomiss Gee, Nafisa Abdullahi, Baballe Hayatu dadai sauransu sun taya Hafsat Alhinin Rasuwar mahaifin nata inda sukai mai fatan Samun Rahama.

Muna anan muna fatan Allah ya jikansa ya sawa abinda ya bari Albarka ya kuma basu juriyar Rashinsa. Amin




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment