Pages

Tuesday 10 December 2019

Masu nada Sarki a Kano sun Maka Gwamnatin jihar da Majalisa a Kotu kan sabbin Masarautu

Masu nada Sarki a Kano sun maka gwamnatin jihar da majalisa a kotu, suna neman kotun ta taka wa gwamnatin jihar burki daga daukar duk wani mataki a kan sabuwar dokar masarautu ta jihar da gwamna Ganduje ya rattaba wa hannu a makon jiya.


Masu shigar da karar dai sun hada Madakin Kano da Makama da Sarkin bai da sarkin dawaki mai tuta.

Hakan dai na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnan ya sanar da nada Sarki Sanusi a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.

Wadanda ake karar sun hada da kwamishinan shari'a na jihar da sabbin sarakunan da aka nada guda hudu.
BBChausa







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment