Pages

Monday 9 December 2019

Ya ji Dala>>Tauraron Fina-Finan Hausa, Zaharadeen Sani ya bayyana kan ziyarar Malaman Izala ga Atiku Abubakar


Bayan da shugabannin kungiyar Izala suka jewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na zaben 2019 a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta'aziyyar rasuwar da aka masa, lamarin ya dauki hankula sosai.



Hotunan ziyarar sun watsu sosai a shafukan sada zumunta inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi kai.

Tauraron fina-finan Hausa, Zaharadeen Sani, Owner ma ba'a barshi a baya ba.

Inda ya saka hoton gaisawar da Sheikh Kabir Gombe yayi da Atiku a shafinshi na Instagram ya rubuta cewa "Ya Ji Dala"

Lamarin ya dauki hankula sosai inda wasu suka goyi bayanshi wasu kuwa cewa suka yi bai dace ba musamman lura da cewa malamai ne.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment