Pages

Monday 9 December 2019

Za'aci gaba da biyan tsokon gwamnan Abia da kotu ta daure bayan kamashi da laifin samada da fadi da Biliyan 7 Albashin sanata

Sanata Orji Kalu wanda yanzu haka ya ke gidan yari zai ci gaba da karbar albashi da sauran hakkokinsa kamar kowane sanata.


Mai magana da yawun majalisar dattawan kasar, Sanata Godiya Akwashiki ne ya shaida wa jaridar PREMIUM TIMES ranar Lahadi.

Sanata Akwashiki ya kara da cewa duk da an samu mista Orji Kalu da laifi kuma an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso, har yanzu sanata ne kuma zai ci gaba da karbar albashi da sauran hakkokinsa.

Ya kara da cewa idan dai har ba kotun koli ce ta yanke hukuncin karshe ba kan dan majalisar dattawan ba to Orji zai ci gaba da kasancewa sanata.

Sai dai kuma mai magana da yawun majalisar ya ce kasancewar Orji Kalu sanata ba ya nufin zai rinka halartar zaman zauren majalisar ba.
BBChausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment