Pages

Monday 9 December 2019

Saudiyya ta daina tilasta raba mata da maza wajan ma'amula

Daga yanzu kasar Saudi Arabia ba za ta kara tilasta wa gidajen abinci su bambance kofofin shigar maza da na mata ba, a wani mataki na kawo sauyi a kan lamuran nishadi.


An ganin wannan wani bangare ne na sassauta dokokin hulda tsakanin jinsin maza da na mata, a kasar domin kasar ta kara samun karbuwa a idanun duniya musamman kasashen Turawa.

Gwamnatin Saudiyyar ta rubuta a Twitter cewa: ''Daga yanzu ba dole ba ne rabe kofar shiga ta maza da kuma ta mata a gidajen cin abinci da ma sauran wuraren da jinsunan biyu ka iya haduwa.


Tun da dadewa daman masu shaguna ko wuraren cin abinci na kasuwa a ka'ida sai sun samar da kofofin shiga wuraren na maza daban da na mata, ga duk wata tawagar iyalai da ta je wurin, don kauce wa haduwar maza da mata.


A cikin wuraren akwai shamaki ko shinge na gilashi da ake sanya wa wanda ke hana haduwar maza da mata wuri guda ko da kuwa a tare suke ko iyalan gida daya ne.

Wannan tsari a yanzu dai tun daga shekara daya ko biyu da ta gabata aka fara ganin sauyinsa, ta yadda wuraren sayar da abincin suka daina yin wannan shamaki.

Baya ga wannan sassauci yanzu kuma kusan a ce an daina ganin jami'an tsaro na Hisbah da ke tilasta bin dokokin Musulunci sau da kafa, a kan titunan kasar, wanda hakan wata alama ce da ke nuna irin sauye-sauyen da Saudiyyar ke aiwatarwa na barin tsauraran dokokinta.

Ana ganin wannan mataki a matsayin karin wata hanya da kasar ta dauka daga irin sauye-sauyen da ta sanya a gaba, bayan irin sukar da ake mata kan murkushe 'yan hamayya inda babban misali na baya bayan nan shi ne mummunan kisan gillar dan jarida Jamal Kashoggi.

A shekarar da ta gabata ana zargin gwamnatin Saudiyyar da hannu a kisan dan jaridar nan Jamal Kashshoggi, a ofishin jakadancin kasar da ke Santambul.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment