Pages

Sunday 19 January 2020

An gargadi 'yan Najeriya kan shan garin kwaki

Daraktan hukumar kiwon lafiya na jihar Enugu, Boniface Okolo ya gargadi 'yan Najeriya akan shan garin kwaki wanda yace zai iya kasancewa yana dauke da cutarnan da ake dauka daga wajan Beraye watau Zazzabin Lasa.





Boniface yace Bera na yawan ta'ammuli da garin kwaki shiyasa suke kira ga mutane da su gujewa amfani da Garin Rogo da ake jikawa da ruwan sanyi a sha tunda ba'a dafashi, kamar yanda ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN.

Ya kara da cewa yin teba da garin kwaki na kashe cutar tunda ana dafashine.

Yace suna yin dukkan me yiyuwa wajan ganin sun dakile yaduwar cutar da kuma sauran cututtuka inda suka kokarin ganin ana ajiye kayan abinci yanda ya dace da kuma dafasu yanda ya dace.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment