Pages

Sunday 19 January 2020

An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun

Mai Shari'a Jide Falola na Babbar Kotun Ikirun da ke jihar Osun a Najeriya ya yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Juma'a bisa laifin kisan kai.


Falola ya ce lauyan mai shigar da kara ya gabatar da cikakkun hujjoji kan Orisakunle Abiodun mai shekara 21 da kuma Opadokun Olayinka mai shekara 29, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN kasar ya ruwaito.

Alkalin ya yanke wa masu laifin hukuncin shekara biyar bisa laifin hada baki da kuma hukuncin rataya bisa laifin kisan kai.


Sai dai kuma Falola ya wanke mutum na uku da ake zargi mai suna Femi Aroyehun sakamakon rashin gamsassun hujjoji a kansa.


Masu laifin wadanda aka fara shari'arsu a ranar 22 ga watan Yunin 2018, sun musanta zargi biyun da aka yi masu na hada baki domin yin kisan kai da kuma aikata kisa.

Tun da farko lauya mai shigar da kara Philips Afolayan ya fada wa kotun cewa mutum ukun sun kashe wani mai suna Matthew Adeoye a ranar 9 ga watan Maris na 2017 a garin Ikirun na jihar Osun.

Afolayan ya ci gaba da cewa daya daga cikin masu laifin, Abiodun ya yi amfani da babur dinsa ne, inda ya bige marigayin a lokacin da yake dawowa daga wurin aiki.

Ya ce hakan ne ya jawo hatsaniya tsakanin marigayin da kuma mutum ukun, abin da ya sa suka lakada masa duka kuma ya mutu a ranar bayan an kai shi asibiti.

Lauya mai kare masu laifin Mista L.S. Bello ya nemi kotu da ta saukaka wa wadanda aka yanke wa hukuncin.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment