Pages

Sunday 19 January 2020

Tsadar rayuwa ta kara kamari da kashi 11.98 a Najeriya

Tsadar rayuwa tare da tashin farashin kayayyaki sun yi tashin da watanni 19 baya ba su yi kamar sa ba.


Farashin kayayyakin masarufi da na abinci sai kara hauhawa ya ke yi, tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakokin kasar nan.

Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa, NBS, ta bayyana cewa tashin tsadar rayuwa zuwa kashi 11.98 a cikin watan Disamba, daga 11.85 cikin watan Disamba, 2019.

Wannan bayani ya fito ne daga NBS a yau Juma’a.

Najeriya ta kulle kan iyakokin ta cikin watan Satumba, wanda hakan ya haddasa tashin farashin kayayyaki.

Hukumar NBS ta ce farashin kayan masarufi sun yi tashin gwauron jirgin sama zuwa kashi 14.67 a cikin watan Disamba, 2019, idan aka kwatanta da yadda farashin ya ke kashi 14.48 a cikin watan Nuwamba, 2019.

“An samu karin farashin sunkin biredi, serelak na jira-jirai, nama, kifi, mai da sinadarai da dama.

Sannan kuma doya ta kara tsada, haka tumatir da rogo da sauran su.”

“Idan wannan wata kayan masarufi sun kara kudi, to wata na gaba ma tsadar dai suke karawa. Kamar yadda watan Nuwamba da na Disamba, 2019 suka nuna.”

Har ila yau, rahoton ya kara da cewa tun da shekarar 2019 ta kama, farashin sai kara hauhawa ya ke yi, musamman ma bayan rufe kan iyakokin kasar nan da Najeriya ta yi.

Tsadar kayayyaki ta fi kamari a jihohin Sokoto, Ogun da Filato a kididdigar karshen shekara. Amma jihohin Bauchi, Delta da Bayelsa, su abin bai shafe su sosai ba.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment