Pages

Saturday 25 January 2020

An yi garkuwa da wani babur a Kano kuma an bukaci kudin fansa

Wanda ake zargin ya dai dauki babur din ne roba-roba kirar Lifan ya kuma ga takardun makarantar mai baburdin a cikin akwatun ajiye kaya wato (booth) harda lambar waya a cikin babur din nan ta key a kuma dauki lambar ya buga ya kirawo mai babur din inda ya nemi a bashi kudin fansa Naira dubu goma sha biyar (15,000) kafin ya bada babur din.


Lamarin da ya sanya nan ta ke mai babur din mai suna Ibrahim ya nemi mai garkuwa da babur din ya bashi lambar asusun san a banki, bayan ya tura kudin a ka sanar da jami’an tsaro suka bibiye shi wato (tracking) din asusun bankin a ka kuma sami nasarar kama shi a Sabon Gari Bata a jihar Kano.




wata abokiyar aikin Ibrahim wacce suka yi waya da wannan matashin da ake zargi da garkuwa da babur din ta ce” A matsayin mahaifiyar Ibrahim na je wa mai garkuwa da babur din amma ya ce shifa balaifin sa bane”.

Sai dais hi mamallakin babur din Ibrahim ya ce “To da ya ke hausawa na cewa rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya, kuma idan daraban shan duka bari bata magani, ashe asusun bankin wani mai sana’ar bada kudi na turawa wato (POS) na karbo wanda kuma ba mu da alaka ta sanaiya da shi”. Inji Ibarhim.

Bincike dai ya tabbatar da cewa wannan matashin mai garkuwa da babur ya siyar da babur din a kan kudi Naira dubu goma shabiyar, duk da dai kokarin da mukayi na zantawa da wannan matashi al’amari ya faskara, dafatan Allah ya tsari gatari da sarar shuka.


Wakilimmu Mu’azu Musa Ibrahim yarawaito cewa, babur din an siyar da shi ne a kasuwar farm center dake Kano, bayan tarkon da aka danawa matashin na farko a ka kuma kara kama wani matashin wanda shi ma ya siyar da babur din, tahanyar.

Dubun dayan matashin ya cika ne bayan wanda ake zargin na farko ya buga masa waya ya sanar da shi cewa an samu wanda zai kara siyan baburin a kan kudi naira dubu arba’in (40000) duk da sun siyar da babur din suka sake zuwa da niyar karbar wannan kudi naira (40000) domin karawa a kan wancan dubu (15000) baya ga dubu (15000) din da suka nemi kudin fansa tun da farko.
DalaFM





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment