Friday, 24 January 2020

Dan Marigayi Musa Dan Kwairo yawa General BMB kyautar tsaleliyar Mota

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhamad Belli da aka fi sani da General BMB ya samu kyautar mota daga dan gidan shahararren mawakin Hausa, Marigayi Musa Dan Kwairo watau Ibrahim Musa Dan kwairo.BMB ya bayyana hakane a shafinshi na sada zumunta inda yace duk da Ibrahim ya ce masa dan Allah ya mai kuma karya saka amma ya sakane dan masoyansa su mai adu'a.

Muna fatan Allah ya tsare.

Ga sakon daya rubuta kamar haka:

"DUKKAN GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH, DUKKAN YABO SUN TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)
Masoyana maza da mata, ina rokonku da ku tayani godiya wajen ALHAJI IBRAHIM MUSA DANKWAIRO (Sarkin Samarin Tafa) (Garkuwan Marayu) (Gatan talakawan Nigeria) (Mai taimakon Al'umma) don KYAUTAR WANNAN BABBAR MOTA DA YA BANI.

Bamu taba haduwa ba, bamu taba magana ko ta waya ba, ban taba zuwa sana'a gidanshi ba sai wannan karo da nazo aikin film garin Abuja, ya samu labari, ya gayyace ni da nazo nayi sana'a a gidan sana'arshi dake TAFA. Cikin gaggawa na amsa kira na tafi TAFA, nayi performance har kwanaki biyu saboda mutunta kowa da yakeyi duk da cewa ALLAH ya hore mishi arziki
Koda baka san ALHAJI IBRAHIM MUSA DAN KWAIRO BA TO KASAN MAHAIFINSHI MARIGAYI MAI SUNA ALHAJI MUSA DAN KWAIRO WANDA HAR YANZU WAKOKIN SU BASU BACE BA KUMA DATTIJAI BASA JIN WASU WAKOKIN SAI IRIN NASU.

Daga karshe, ina yiwa kowa addu'a da ALLAH ya hore ma wadanda basu dashi fiye da wanda aka bani, wadanda suke dashi kuma ALLAH ya kara musu, shi kuma wannan bawan ALLAH mai kyauta domin ALLAH wanda yace don ALLAH yayi kar nayi posting, ni kuma nayi posting don masoyana su masa addu'a 🤲🤲🤲 da kyawawan bakunansu masu ALBARKA."
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment