Pages

Monday 27 January 2020

Direban Sardauna Ya Bukaci Tambuwal Ya Siya Mishi Gida

Alhaji Shehu Aliyu Maradun dattijo dan shekaru 74 shine direba na biyu ga Firimiyan Yankin Arewa, Sa Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) har zuwa kisan gillar da aka yi masa a ranar 15 ga Janairu 1966. 


Tsohon direban na Sardauna a yayin tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU a wannan lokacin da Gamji Dan Kwarai ya cika shekaru 54 da kisan gillar da makiya ci-gaban kasa suka yi masa ya bukaci alfarma ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da ya taimaka ya biya masa kudin gidan gwamnati da yake ciki a tsawon shekaru 29. 

Direban na Sardauna yana zaune ne a cikin Rukunin gidajen da aka fi sani da ‘Line G’ a unguwar Guiwa wadanda suna daya daga cikin gidajen da Gwamnatin Sakkwato ta baiwa ma’aikatan da ke ciki da wadanda suka yi ritaya damar mallaka a shirinta na kyautatawa ma’aikata. Ya ce aikin da suka yi da Sardauna ba su yi shi domin tara dukiya ba. 

“Zamanmu da Sardauna mun horu da aiwatar da alheri da gaskiya da adalci tare da yi domin Allah. Haka ma bayan rasuwarsa mun ci-gaba da rike matsayin mu domin ba mu taba amfani da sunan Sardauna domin neman abin duniya ba.” Inji shi. 

A watan Satumban 2018 ne Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umurnin sayar da Gidajen Gwamnati 1, 497 da ke unguwannin Guiwa, Bado, Arkilla Nasarawa, Runjin Sambo da gidajen Gwamnati a GRA ta Yammaci da Gabascin Sakkwato tare da bada dama a bisa ga adalci na Gwamnati ga wadanda ba ‘yan jiha ba amma kuma sun yi wa Gwamnatin jiha aiki da su mallaki gidajen. 

Kashi 90 cikin 100 na gidajen ne kwamitin musamman a karkashin Kwamishinan Gidaje a wancan lokacin Hon. Bello Abubakar Guiwa ya bayar da shawarar siyarwa. 

“Ina zaune cikin gidan mai dakuna biyu da iyali na yau shekaru 29, ina kuma da ‘ya’ya 20. Gwamnati ta yi wa gidan kudi naira Miliyan 2.5 kuma ba ni da karfi da halin sayen gidan domin kudin fanshon da ake biya na ba su ko kai naira dubu 5, 000 ba. Don haka ina neman arziki ga Gwamnan mu mai gaskiya da adalci Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Babanmu Mai Alfarma Sarkin Musulmi da su taimaka mani su biya mani kudin wannan gidan da nake zaune a ciki.” Ya bayyana. 

Jikan na Sarkin Kayan Maradun, Muhammadu Moyi ya bayyana cewar bayan rasuwar Sardauna wanda shine ya yi masa auren farko ya dawo gida Sakkwato da aiki a ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, bayan kirkiro Jihar Zamfara kuma ya koma can da aiki a inda ya yi ritaya a 2007. 

“Ina cikin gida mai lamba G 11 a Rukunin Gidaje 54 na ‘Line G’ tun a lokacin da ake biyan hayar gidajen naira 31 kacal. A bisa ga karimci, adalci da dattakon Gwamna Tambuwal da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ina rokon Gwamnati da Majalisar Mai Alfarma su duba matsalar da nake ciki su kuma share mani hawaye na.” 

“A bisa ga zaman da na yi da Sardauna, ina rokon Gwamna Aminu Tambuwal da Baba na Sarkin Musulmi a bisa ga adalcinsu da sanin ya kamata, su kalli kima, martaba da mutuncin wanda na yi aiki a karkashinsa, su taimaka mani in mallaki wannan gidan.” 

Ya bayyana cewar a wannan lokacin da ake jimamin cika shekaru 54 da rasuwar Sardauna, suna kewar rabuwa da shi, suna kuma kishiryar samun kyakkyawan shugabanci mai tattare da adalci da wanzar da zaman lafiya irin na Sardauna wanda ya bayyana cewar ya rayu rayuwa tagari ya kuma koma ga mahallaccinsa a lokacin da kasa da ‘yan kasa ke bukatarsa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment