Pages

Monday 27 January 2020

Kobe Bryant da 'yarsa sun mutu a hadarin jirgi

Fitaccen dan wasan kwallon kwando Ba'amurke Kobe Bryant na daga cikin mutane biyar da jirgin helokofta da suke ciki ya yi hadari a birnin Calabasas na California.


Rahotanni sun bayyana cewa jirgin da Bryant, mai shekara 41 ya ke ciki ya fado ne tare da kamawa da wuta.

Ana yi wa dan wasan kwallon kwando da ya ke rike da kambu biyar na NBA kallon gawurtacce da duniyar wasan kwallon kwando ba za ta taba mantawa da shi ba a tarihi.




Tuni fitattun mutane ciki har da takwarorinsa na wasanni daban-daban suka fara aikewa da sakon alhini da jimamai da kuma ta'aziyyar babban rashin da suka yi.

Yawanci sun bayyana kaduwa da mutuwar fuju'ar da Kobe ya yi.


Dan wasan kwallon kwando Kevin Love ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter cikin kaduwa ya na cewa ''Dan Allah kar ku fada min haka, ku ce ba gaskiya ba ne. Kai wammam labarin ba gaskiya ba ne.''

Shi ma shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ''Mummunan labari.''

Kawo yanzu ba a fitar da sunayen mutane hudu da suka mutu tare da Bryant ba.


Kobe ya shafe duka shekaru 20 a matsayinsa na kwararren dan wasa kwallon kwando a kungiyar Los Angeles Lakers, ya kuma yi ritaya a watan Afrilun 2016.

Nasarorin da ya yi sun hada da karbar kambun dan wasan NBA mafi kadari har sau uku.

Hakama ya lashe babbar gasar kwallon kwando sau biyar duk da kungiyar Los Angeles Lakers.

Baya ga nasarorin da ya samu a kwallon kwando, Kobe Bryant ya fito a fina-finai, kuma anan ma ya taba lashe kyautar Oscar a wani fim mai suna Dear BasketBall a shekarar 2018.
BBChsusa.






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment