Pages

Thursday 23 January 2020

Ina so in zama kamar Cristiano Ronaldo>>Mbappe

Tauraron dan kwallon kungiyar PSG,Kylian Mbappe ya bayyana cewa yana so ya zama kamar Ronaldo a harkar kwallon kafa.




Dan asalin kasar Faransa ya bayyanawa manema labarai cewa, duk wanda ya taso a kasar Faransa, Zidane ne gwaninsa kuma shima hakan take a gurinshi.

Saidai yace wanda yake kallo yake kara mai gwarin gwiwa a harkar kwallon kafa shine Cristiano Ronaldo kuma yana so yayi bajinta irin tashi.

Da aka tambayi Mbappe Messi fa? Sai yace ai ya makaro da son zama kamar Messi dan tun farko Ronaldo ya kama.



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment