Pages

Saturday 18 January 2020

Ji yanda wani dalibi yawa Boko Haram Wayau suka sakeshi bayan da suka yi garkuwa dashi

Wani dalibin jami'ar Maiduguri dake jihar Borno, me suna Mu'umain Muhammad yawa kungiyar Boko Haram wayau ta sakeshi bayan garkuwa da suka yi dashi.


Rahotanni sun bayyana cewa tsakanin Ranar Talata da Alhamis ne 'yan boko Haram din suka sace wasu dalibai 8 akan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri kuma Mu'umain na ciki wanda aka sace

Saidai a kokarin tsira daga hannun 'yan Boko Haram din dalibin ya musu karyar cewa yana karantar Larabcine a jami'a dan ya kammala ya fara wa'azi, kamar yanda The Cable suka ruwaito.

Dalilin haka kuwa tasa Boko Haram din ta saki matashin dalibin yayinda ta ci gaba da tsare sauran daliban data koma.

Kokarin jin ta bakin soji ko jami'ar Maiduguri ya ci tura.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment