Pages

Sunday 26 January 2020

Jihar Kaduna ta tabbatar da Bullar Zazzabin Lasa

BULLAR CUTAR LASA A JIHAR KADUNA

An samu tabbacin bullar cutar lasa a Jihar Kaduna kuma wanda ya kamun wani ne namiji dan shekara 36 daga Karamar Hukumar Chikun.


Tuni dai aka gano shi kuma aka fara ba shi kulawa ta musamman a kebabben wurin kulawa da cututtuka masu yaduwa. 

Wannan dalilin ne ya sa ma’aikatar lafiya ta yi kira ga jama'a su kula da tsafta sannan su hanzarta kai rahoton duk wani alamun cutar ta Lassa ga asibiti mafi kusa.

A cikin sanarwan da ke dauke da sa hannun kwamishiyar kiwon lafiya ta Jihar  Kaduna Dakta Amina Baloni ya nuna cewa an sanya dukkan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati a cikin shirin-ko-ta-kwana domin dakile bulla da yaduwar cutar.

Bincike da gwajin da aka yi sun tabbatar da cewa cutar ce ta harbi wanda aka gano a Karamar Hukumar Chikun dan shekaru 36.

Tuni ma’aikatar ta lafiya ta samar da jami’ai da kayan aiki a cibiyoyin kiwon lafiya domin dakile yaduwar cututtuka inda ake zaune cikin shirin-ko-ta-kwana sannan cibiyoyin zasu kasance a bude domin ba da kulawar gaggawa.

Ana dada jan hankalin jama’a da su kula da tsafta sannan su killace abinci da abin sha kuma su sanya ido tare da kai rahoton duk wanda ake ganin ya harbu da cutar ga hukumomin da suka dace.

Da zarar an ga mai alamun cutar sai a kai rahoto ga bangaren cututtukan annoba ko kuma a kira lambobin wayar nan: 08036045755 ko kuma 08027396344 ko a sanar da cibiyar kiwon lafiya ta karamar hukuma.

Mu hada hannu domin kare jiharmu sannan mu gaggauta kai rahoto domin wadanda suka kamu su samu kulawa a kan lokaci.

Sa Hannun 
Dakta Amina Baloni
Kwamishiniyar Ma’aikatar Lafiya
25 ga Janairu 2020







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment