Pages

Sunday 26 January 2020

Ko nawa za'a biyani ba zan iya fitowa a fim ina lalata da mace ba, saidai Kiss da Runguma>>Sani Musa Danja

Tauraron fina-finan Hausa,Sani Musa Danja, Zaki ya bayyana cewa a lokacin da ya taso yana son yin rawa da Waka, Mahaifansa sun ce dole ya dage da Karatu ifan yana so a barshi yayi sana'ar tashi.




Danja ya bayyana hakane a hirar da Punch ta yi dashi inda yace tun yana Yaro ya fara Rawa da Waka. Yace yakan bi Abokanshi zuwa Coci sannan auma su bishi zuwa Masallaci a wancan lokacin.

Da yake magana akan yin fim a Yanzu,Danja yace Ya fi yin Fina-finai da wakokin Turanci fiye dana Hausa.

Ya kuma ce al'ada da ra'ayin 'yan mazan Jiya da Arewa take dashi ne yasa wasu 'yan fim din Arewar basa son zuwa Kudu su yi fim saboda akwai abubuwan da bazasuniya yi ba kamar taba mata.

Da yake Magana akan Kanshi, Danja yace Shima dai ko nawa za'a bashi ba zai iya fitowa a fim yana Lalata da wata ba amma dai zai iya yin Kis da kuma Runguma, yace yama yi hakan a baya.

Da yake amsa Tambaya akan ko zai iya komawa Legas da zama?

Danja yace gaskiya da kamar Wuya wanda ya fito daga Arewa ya koma Legas da zama dindindin. Yace duk da yana shiga Legas akai akai amma baya sha'awar komawa can da zama. Abinda kawai yake so shine zai gina Gida acan ta yanda idan yaje ba sai ya rika kama Hotal ba.

Danja yace yana tare da 'yan Siyasa amma baya sha'awar shiga Siyasar amma yakan baiwa wanda yake ganin zai Amfanawa Al'umma goyon baya sanan baya zuwa Maula idan wanda ya goyawa baya ya samu mukamin.

Ya kara da cewa bayan Fim da waka yana da sana'ar sayar da mota da kuma gidan Daukar hoto da sauran wasu hanyoyin samun kudi.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment