Pages

Saturday 25 January 2020

Kungiyoyin Boko Haram Biyu sun gwabza Mummunan fada tsakaninsu

Kungiyoyin Boko Haram biyu na ISWAP data balle daga jikin Asalin Boko Haram din da Shekau ke jagoranta da Bangaren Shekau din ta Asalin Boko Haram sun gwamba mummunan fada tsakaninsu da yayi sanadiyyar mutuwar 'yan kungiyar da dama.



Wata majiya ta kungiyar ce ta kwarmatawa kamfanin dillancin labarai na AFP da wannan labari inda tace Bangaren Shekaune suka kaiwa ISWAP hari dan kwato wasu mata da ISWAP din ta kwace musu.

Ranar Larabar data gabata ne aka yi wannan kazamin yaki inda Rahotanni suka bayyana cewa kowane bagare ya ji jiki. Saidai Bangaren Shekau din basu samu damar kwace matan nasu ba.

A kwanakin baya ne dai ISWAP ta kaiwa bangaren Shekau hari inda ta kwace wasu mata 13.

ISWAP wadda itace kungiyar Boko Haram da kungiyar IS ta sani kuma ta amince da ita a matsayin wakiliyarta a yankin Africa ta Yamma ta balle daga Asalin Boko Haram ne saboda inkarin kaiwa fararen hula hari da Shekau ke yi da kuma kashe kwamandojin Yakinshi da yake yi da zarar sun bayyana ra'ayin da ya banbanta da nashi.

Mabiya wannan kwamandoji sun rika komawa bangaren IS inda sukace ba zasu yafe kisan da Shekau yawa jagororin nasu ba.

Kowane bangare tsakanin kungiyoyin biyu na kafurta juna.

A kwanakin bayane tawagar wasu kungiyoyin kasashen Mali da Libya suka zauna da bangarorin biyu na Boko Haram dan sasantasu amma abin ya faskara.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment