Pages

Saturday 25 January 2020

Barcelona ta sha kashi a hannun Valencia da ci 2-0: Golan Barca yayi kokari soosai

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sha kashi a hannun Valencia da ci 2-0 a wasan da suka buga na gasar cin kofin Laliga a yau.





Bayan dawowa daga hutun rabin lokacine Jodi Alba ya ci kungiyar tashi ta Barca bisa Kuskure sannan kuma ana kusa da tashi daga wasan Valencia ta kara likawa Barca kwallo daya. Messi ya zubar da dama me kyau.

Suarez be buga wasan na yau ba inda Ansu Fati ya buga wasan da be kayatar ba.

Saidai gaskiya Golan Barca Marc-Andre Ter Stegen  yayi bajinta matuka dan kuma ba dan kokarinshi ba da Barcelona yau an mata cin sai badi kwa rama. Ya tare kwallayen da ya kamata ace sun shiga raga sannan kuma Valencia ta samu bugun daga kai sai gola shima kuma ya tare shi.

Wannan ce rashin nasara ta farko da sabon Kocin Barca, Quique Setien ya fusnkanta inda a wasanshi na farko yayi nasara

Kalli bajintar Ter Stegen a kasa:












Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment