Pages

Sunday 26 January 2020

Man United na neman Dan wasan Najeriya ido Rufe

Kungigar kwallon kafa ta Manchester United a neman tauraron dan kwallon Najeriya, Odion Ighalo ido Rufe dan ya maye mata gurbin dan wasan gabanta, Marcus Rashford da ya tafi jinyar watanni 3.




Sky Sport ta ruwaito cewa Man United ta saka sunayen Odion Ighalo dake bugawa kungiyar kasar China ta Shanghai Shenhua wasa da kuma Islam Slimani dan kungiyar Leicester City da ta baiwa Monaco aro a matsayin 'yan wasan da zata neman su zo mata Aro na dan wani lokaci.

Bayan kammala wasan Man United da Burnley da Man U din ta sha kashi da ci 2-0, kocin United ya bayyana cewa, dolene su samawa kansu waraka ta dan wani lokaci saboda rashin Rashford.

Idan dai komawar Ighalo Man United ta tabbata zai zama dan Najeriya na farko da ya bugawa kungiyar wasa a matsayin babban dan kwallo.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment