Pages

Sunday 19 January 2020

Sai dana cewa 'yan wasana kada su bar Zaha ya rika gudu>>Kocin Man City

Kocin kungiyar Manchester City,Pep Guardiola ya bayyana cewa ya gayawa 'yan wasan bayanshi da kada su bar Zaha ya riga gudu amma suka kasa.



A wasan da suka buga jiya,Man City ta farke kwallon da Crystal Palace ta fara cinta ta kuma kara ta 2 ta hannun Aguero. Saidai ana mintin karshene, Zaha ya bugo wata kwallo data taba kafar Fernandinho ta shiga raga,haka aka tashi wasan 2-2.

A hirar da yayi da ''yan Jarida bayan kammala wasan, Guardiola ya yabawa 'yan wasan nashi saidai yace avu daya daya gaya musu su yi suka kasa yi shine ya jawo musu barin maki, watau kada su bar Zaha ya rika gudu.

Saidai yace zasu gyara kuskuren nasu nan gaba.

City tana matsayi na 2 a saman teburin Premier da maki 48.

Arsenal ma dai bata canja zani ba har yanzu inda wasansu na jiya da Sheffield suka tashi 1-1




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment