Pages

Thursday 13 February 2020

Buhari ya ji ihun da aka masa a Maiduguri: Ji martanin daya mayar

Fadar shugaban Najeriya ta ce ta ji yadda wani rukunin mutane suka yi wa tawagar shugaba Buhari ihu a yayin da ya kai ziyarar jaje a Maiduguri.


Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya ce, wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba wadanda ya ce an san su da karamci da son baki.

"Da ni aka shiga gari tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehu kuma jama'a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka."

"Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so," in ji Garba Shehu.

Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa harin Auno da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Wasu dai na ra'ayin cewa ihun da aka yi wa shugaban manuniya ce kan yadda al'ummar arewa maso gabashin kasar suka fusata da rashin daukar kwakkwaran mataki daga gwamnatin don kawo karshen hare-haren Boko Haram.




Sai dai kuma Garba Shehu ya yi zargin cewa kila wasu 'yan siyasa ne suka tattaro wasu tsiraru aka ba su kudi don su yi wa Buhari Ihu.

Kuma a cewarsa gari kamar Maiduguri, ba za a rasa yawan mutum da ya kai miliyan hudu ba zuwa biyar ba kuma tun da mutum ba Allah ba ne ba zai iya gamsar da kowa da kowa ba.

Ya ce gwamnatin Buhari ta nuna za ta iya yaki da Boko Haram kuma shugaban ya yi alkawalin canza matakan yaki na magance abin da ya kira sabuwar matsalar da aka samu.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

Harin da aka kai Auno ya fusata mutanen Borno, inda da dama suka zargi jami'an tsaro da sakaci bayan sun rufe hanyar shiga Maiduguri da yammaci, dalilin da ya sa mayakan Boko Haram suka riske matafiya a cikin dare.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment