Pages

Thursday 13 February 2020

RAHOTON MUSAMMAN: An fallasa yadda Diya, Aziza da Magashi suka tafka satar bilyoyin nairori

Rahotannin musamman sun bayyana yadda wasu manyan sojoji a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha, suka bi sahun sa wajen jidar bilyoyin kudaden al’umma su na maidawa na su.


Daya daga cikin wadancan manyan sojoji da a yanzu Minista ne a gwamnatin Buhari, wato Bashir Magashi, sun rika jidar kudaden su na kimshewa a kasashen waje ta hanyar tsarin bankin kasa da kasa, a wata harkalla irin ta ‘Da’u fataken dare.

An rika boye kudaden a kasashen waje daga cikin kudaden danyen mai da aka rika kwasa a boye, bisa sa hannun Abacha, shugaban da Kungiyar (Transparency International) ta bayyana cewa ba taba yin rikakkun barayin shugabanni ba, kamar shi da Suharto na Indonesia da kuma Mobuto Sese-seko na Zaire, wadda a yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

An kiyasta cewa Abacha ya saci akalla dala bilyan 3.5 daga baitilmalin Najeriya.

Jigilar Kudaden Sata Daga Najeriya Zuwa Waje

Wani salo shugabannin lokacin a karkashin sahalewar Abacha suka yi, suna boye kudaden cinikin danyen man fetur da aka rika fitarwa a cikin wani asusun ajiya na sirri.

Wani rahoto da aka gudanar lokacin mulkin Obasanjo na farar hula a zangon farko ya nuna, Manjo Janar Patrick Aziza a lokacin da Manjo Janar Magashi wanda a yanzu Ministan Harkokin Noma ne, suka rika amfana da kudaden satar da aka rika dirkawa a zamanin mulkin su.

Obasanjo ya dauko hayar wani Bature kwararre wajen iya bincike mai suna Enrico Monfirini, kuma kwararren lauya cikin 1999.

Monfirini ya gano makudan kudaden da suka sata, kuma cikin fushi Obasanjo ya umarci Mashawarcin sa kan Tsaro, Sarki Muktar cewa ya tilasta su maido wannan tulin kudade da suka wawura.

Jinkai Da Obasanjo Ya Yi Musu

Obasanjo bai daure su ba, sai ya ce su maida dukiyar da suka wawura.

An gano Aziza ya kimshe makudan kudade a asusun boyon kudaden sata da ya bude a bankin Tsibirin Jersey na BNP Paribas a reshen sa na Birtaniya.

Haka dai rahoton da Sarki Muktar ya yi lokacin Obasanjo ya bayyana, mai lamba NSA/A/223/1/C ya tabbatar

Rahoton ya ci gaba da fallasa sauran manyan janar din da aka bayyana sunan su a sama.

Duk da cewa Obasanjo ya yi wa Aziza afuwa da daga kafar rage masa adadin kudaden da zai maida, sai ya kira amsa kiraye-kirayen da Ofishin Sarki Muktar ya rika yi masa.

Wannan ya ba Obasanjo haushi, har ya rubuta wa Sarki Muktar wasika ya umarce shi, “A sa EFCC su gaggauta kama Janar Aziza, a tuhume shi, kuma a tilasta sai ya maido kudaden da ya sata.

Aziza na cikin manyan ‘yan barandan sojojin da suka yi wa Shonekan juyin mulki tare sa Abacha. Kuma shi ne Shugaban Kwamitin Binciken Zargin Juyin Mulkin da aka ce Obasanjo sun shirya a 1995.

Obasanjo har ila yau ya umarci, ” a kwato kudaden da Diya ya sata kafin 31 Ga Disamba, 2006.

Yadda Magashi Ya Tsallake Siradin Tonon Silili

Shi kuwa Magashi, wato Ministan tsaro yanzu a karkashin Buhari, sai ya nemi a rufa masa asiri, ya maida dala 400,000 daga cikin dala 550,000 da ya wawura. Sai aka bar masa sauran dala 150,000 aka ce ya rike ya sha miya.

Duk da wannan dirkaniya ta Magashi, hakan bai hana Buhari ya kinkimo shi ya nada shi minista ba.

Kamar dai yadda shi ma Gwamnan Jihar Kebbi na Yanzu, Atiku Bagudu, duk da harkallar fitar da kudaden Abacha, hakan bai hana shi zama sanata da gwamna ba a kasar nan.

Premiumtimeshausa






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment