Pages

Friday 14 February 2020

Har yanzu Ighalo na killace a Man United saboda Coronavirus

Dan wasan da Manchester United ta saya a karshen watan Janairu, Odion Ighalo na yin atisaye shi kadai a makon nan.


Hakan na daga cikin matakan kariya, bayan da ya koma Old Trafford daga China.

United ta dauki wannan matakin ne don gudun yada coronavirus wadda asalinta daga China.

Kungiyar ba ta je da shi atisayen da ta yi a Spaniya ba, saboda tana tsoron hana shi takardar izini musammam idan za su koma Burtaniya.

Dan kwallon Nigeria, ya koma United wadda zai buga wa wasannin aro zuwa karshen kakar bana daga Shanghai Shenhua ta China.




Ighalo mai shekara 30, yana cikin 'yan wasan da Ole Gunnar Solkjaer ya ce za su buga masa karawa da Chelsea a gasar Premier ranar Litinin.

BBC ta fahimci cewar Ighalo yana yin atisaye shi kadai tare da taimakon United domin ya koma kan ganiyarsa, yadda zai fuskanci Chelsea da kwarin gwiwa.

Yana kuma yin atisayen ne a katafaren cibiyar Taekwondo na kasa kusa da filin Etihad, kuma inda yake da zama tun komawarsa Ingila kwana 11 da ya gabata.

Ma'aikatar lafiya ce ta sanar cewar a killace duk wani matafiyi kwana 14 da zai shiga Burtaniya daga wasu kasashe da ta lissafa har da China.

Mutanen da suka mutu sakamakon coronovirus sun kai sama da 1,350 da kuma mutum 60,000 da suka kamu da cutar.

An soke wasu wasanni da dama sakamakon tsoron yada cutar.
BBC




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment