Pages

Friday 14 February 2020

Matsalar Tsaro: Kungiyar Izala ta bukaci Malamai da su yi Addu'o'i a Masallatan Juma'a

Kungiyar wa'azin musulunci, mai kira da tsaida sunnah, da kawar da bidi'ah ta jama'atu Izalatil Bid'ah wa iqamatis Sunnah ta tarayyar Niijeriya, ta umurci limamai a dukkan masallatan Juma'a dake fadin Nijeriya, da su yi addu'oi na musamman a karshen hudubobin da za su gabatar a Juma'ar nan, da sauran Jumu'ar da za su biyo baya har zuwa lokacin da za'a dakatar akan wannan musiba da ta addabe mu na kashe kashen mutanen da ba su ji ba basu gani ba. 


Kiran ya fito ne daga bakin shugaban IZALA na kasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a zantawa da 'yan jaridu da yayi a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja. Shehin Malamin ya kara dacewa, umurnin zaici gaba da aiki a duk lokacin da za'a gabatar da sallar juma'a har na tsawon lokaci. Haka zalika Shugaban ya umurci Limamai na kamsul-salawat a dukkan masallatan dake fadin kasa da Su dukufa da addu'oi ta hanyar karatun al-qur'ani da azkarai a masallatan su domin neman Allah ya zaunar da kasar mu lafiya. 

Sheikh Bala Lau yaci gaba da jan hankalin jama'a kan yawaita tuba daga Manyan zunubai, da yawaita istigfari. Sannan mawadata su dinga yin sadaka da tallafawa Marayu. Haka zalika suma Shugabanni su ji tsoron Allah suyi Adalci da jajircewa wajen daukan dukkan tsauraran Matakai wajen magance tabarbarewar tsaro a kasar baki daya. Sannan Yan siyasa suji tsoran Allah kada a sanya harkar siyaya chikin harkan tsaro na wannan kasa, zaman lafiya bukata ce ta kowa" Inji Sheikh Bala Lau. 

A karshe Shugaban ya ce "idan mun yi haka muna sa ran samun ijaba daga Allah Madaukaki Sarki. Allah ya zaunar da mu lafiya, Ya kawo mana karshen wannan kashe-kashe da ya addabe mu a wannan kasa mai tarin albarka".







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment