Pages

Tuesday 2 January 2024

Gajerun sakonnin soyayya

Ga Gajerun sakonnin soyayya masu rasha jiki kamar haka:

 

Duk yadda zuciyata ke tafasa da na ganki sai inji ta yi sanyi.

 

Kece karin kumallo na, ko da na ci abinci in banji muryarki ba yunwa bata sakina.

 

Taba waya akwai dadi amma ni hira dake yafi min dadi.

 

Ko a indiya sai an bincika kamin a samu me kyau irin naki.

 

Bansan akwai mata masu kama da larabawa ba a kasar mu sai da na hadu dake.

 

Bincikena ya kare ban gano mace me kwarjini irin naki ba.

 

Kanshinki na kai Duniyar da ban tantance ba.

 

Nasan 'Ya'yanmu zasu zama kyawawa saboda mun dace da juna.

 

Ni yi babbar sa' idan na sameki a matsayin mata, dan kuwa 'ya'yana zasu samu tarbiyya.

 

Hankalinki da nutsuwarki na kara sawa in soki.

 

Kina da kamun kai, kina da girmama mutane, kin iya kalaman soyayya, Allah yawa iyayenki Albarka dan sun baki tarbiyya me kyau.

 

Idan aka ajje min kudi dake, ke zan dauka.

 

Babu abinda zai sa in daina sonki.

 

Jin Muryarki nasa in samu nustuwa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment