Pages

Monday 26 February 2024

Kalli Hotuna: Sojan kasar Amurka ya kone kansa Kurmus a gaban ofishin Jakadancin Kasar Israela dake kasar inda yace ya gaji da cin zalin da akewa Falasdinawa

Wani sojan kasar Amurkame suna, Aaron Bushnell dan kimanin shekaru 25 ya bankawa kansa wuta.





Sojan ya je kofar ofishin jakadancin kasar Israela dake Amurka ne inda ya bankawa kan nasa wuta.

Ya rika ihun cewa ya gaji da kisan kiyashin da akewa Falasdinawa inda kuma yace a bar Falasdinawa su shaki iskar 'yanci.

Ya ta fadin hakan har jikinsa ya kone ya fadi kasa.

Daga baya an garzaya dashi Asibiti saidai ya mutu.

Kasar Amurka dai itace babbar zugazugin dake baiwa kasar Israela makaman da suke yakar Falasdinawa dasu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment