Pages

Friday 12 April 2024

'An sako ɗaliban jami'ar da aka sace a Taraba'



Ɗalibai biyu daga jami'ar gwamnatin tarayya ta Wukari da ke jihar Taraba da ake zargin masu garkuwa sun sace su sun shaƙi iskar ƴanci.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an saki ɗaliban ranar Alhamis da daddare a kusa da ƙauyen Chinkai da ke ƙaramar hukumar Wukari.

Shugabar sashen yaɗa labarai na jami'ar, Ashu Agya ce ta bayyana hakan ga Channels ta wayar tarho.

A cewarta an biya kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.

Tun farko kafar yaɗa labaran ta ruwaito cewa an sace ɗaliban da ƙarfe 10 na dare ranar 1 ga watan Afrilu a wani wajen cin abinci da ke wajen harabar makarantar.

A ranar da lamarin ya faru, masu garkuwar sun yi ƙoƙarin sace wasu ɗaliban sai dai ba su yi nasara ba abin da ya janyo suka lakaɗawa ɗaliban da masu shagon duka tare da sace kayansu.

Kashi 90 cikin 100 na malamai da ɗaliban makarantar na zama ne a wajen jami'ar kamar yadda shugaban jami'ar ya faɗa a bikin yaye ɗalibai da aka yi a baya-bayan nan.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment