Pages

Friday 12 April 2024

Kotu ta ba da belin Emefiele kan naira miliyan 50



Babbar kotu a Legas da ke zamanta a Ikeja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Mai shari'ah Rahman Oshodi ya bayar da belin tsohon jami'in gwamnatin kan kuɗi naira miliyan 50 tare da gabatar da masu tsaya masa biyu kan irin yawan kuɗin.

Kotun ta kuma ce dole ne mutanen biyu su zama ma'aikata sannan kuma ya zama suna da shedar biyan haraji ta shekara uku tare da gwamnatin jihar Legas.

Alkali Oshodi ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su nuna cikakkun takardun shaida sannan kuma sole ne su yi rajista ƙarƙashin tsarin karɓar beli na gwamnatin jihar Legas.

Alƙalin ya kuma ce ya gamsu da ƙa'idar cika belin ta naira miliyan ɗaya da tun farko aka bai wa Henry Isioma-Omoli wanda shi ma yake fuskantar shari'a kan wata tuhuma gaban alƙali Olufunke Sule-Hamzat na babbar kotun Legas da ke zamanta a Yaba.

A cewar kotun, dole ne a miƙa takardun belin ga kotun da ke sauraron laifuffuka na musamman kuma dole ne a yi rajistarsu a ƙarƙashin tsarin karɓar beli na gwamnatin jihar Legas.

A ranar Litinin da ta gabata ne, hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa ta gurfanar da Emefiele gaban kotu kan zargin tafka laifuka 26 da ke da nasaba da aikata ba daidai ba da kuma karya ƙa'ida wajen fitar da kuɗi da ya kai dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment