Pages

Friday 12 April 2024

Lassa ta kashe mutum 150 cikin jihohi 24 a Najeriya – NCDC

Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka NCDC a Najeriya ta tabbatar cewa cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 150 tsakanin Janairu zuwa Maris ɗin 2024.

NCDC wadda ta fitar da alƙaluman cikin wani rahoto da ta saki ranar Alhamis, ta ce mace-macen sun faru ne a ƙananan hukumomi 125 daga jihohi 27 a Najeriya.

A jumulla, in ji NCDC, daga mako na ɗaya zuwa na 13 na wannan shekarar, mutanen da suka mutu sanadin kamuwa da cutar lassa sun kai kashi 18.6 cikin 100 wanda ya ɗara adadin da aka samu a irin wannan lokaci a bara wanda adadin yake kashi 17.5 cikin 100.

Hukumar ta ce an tabbatar mutum 806 sun kamu da zazzaɓin lassa cikin mutum 5,295 da ake zargi cutar ta harbe su a jihohin da lamarin ya shafa.

A cewar NCDC, kashi 62 cikin 100 an bayar da rahotonsu ne daga Bauchi da Edo da Ondo da kuma Filato.

Sai dai ta ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a mako na 13 na wannan shekarar ya ragu zuwa 15 daga 25 da aka bayar da rahoton a makon da ya gabata.

A cewar rahoton, a jumulla a wannan shekarar, jihohi 27 sun bayar da rahoton aƙalla kamuwar mutum ɗaya da cutar a assan ƙananan hukumomi 125 duk da cewa kashi 62 cikin 100 na duka mutanen da suka kamu da cutar sun fito daga Ondo da Edo da Bauchi yayin da kashi 38 cikin 100 na mutanen suka fito daga jihohi 24 da aka tabbatar da ɓullar cutar lassa.

Cikin kashi 62 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, NCDC sun ce jihar Ondo ta bayar da rahoton kashi 24 cikin 100 sai Edo mai kashi 22 da Bauchi da ke da kashi 16 cikin 100.

A cewar hukumar, galibin waɗanda cutar ta fi shafa ƴan shekara tsakanin 31 zuwa 40 ne.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment