Thursday, 19 April 2018

'Shugaba Buhari beyi maganar batanci ga matasa ba'>>Saeed Nagudu

Tauraron mawakin Hausa, Saeed Nagudu ya bayyana ra'ayinshi akan maganar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi akan matasa inda ya bayyana cewa Buharin beyi maganar batanci ga matasaba.Ga abinda ya bayyana kamar haka:

"KAR JAHILCI YA RUFE MUKU IDO MAKIYA BABA BUHARI MAKIYA NIGERIA ABUN DA SHUGABA BUHARI YAKE NUFI DA JAWABINSA NA LONDON.... Cikin tausayawa da kokarin gyarawa shugaba buhari yace, mafiyawa daga cikin matasan Nigeria, basu samu damar yin karatu mai zurfi ba, wanda hakan yasa Gwamnatocin da sukayi mulki a baya, suke amfani da rashin ilmin matasan suke sanyasu ayyuka marasa kyau, maimakon ace suna aiki ne wanda zasu tallafawa kansu da iyayensu.... Sai yake bayyana cewa tunda yazo kan mulki yake ta kokarin gyara harkar ilmin Nigeria, don haka ya bawa matasan damar samun ilmi mai inganci.... Ko kadan shugaba Buhari baiyi maganar batanci ga matasan Nigeria ba, kawai dai wasu yan siyasa ne suka juya maanar maganar tasa, suke son suyi amfani da hakan don neman biyan bukatar siyasa"

No comments:

Post a Comment