Pages

Tuesday 25 June 2019

Chelsea zata dauki Lampard horas da 'yan wasanta

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu izinin yin magana da kungiyar tsohon dan wasanta Frank Lampard dan daukarshi aikin me horas da 'yan wasanta Daga kungiyar Derby county.



Lampard ya horas da Derby na tsawon kakar wasa daya kuma tsohon dan wasan Chelsea ne da ya kwashe shekaru 13 yana wa kungiyar wasa.

Rahotanni sun bayyana cewa zai sakawa Kwantirakin horas da 'yan wasan Chelsea na shekara 3 hannu idan tattaunawar ta kaya sannan Chelsea zata biya Derby fan miliyan 4 kudin daukar Lampard din.

Ana sa ran cikin sati me zuwane za'a kammala komai.

No comments:

Post a Comment