Pages

Tuesday 25 June 2019

Gamayyar jam'iyyu 60 sun roki Atiku daya hakura da maganar leka rumbun tattara sakamakon zaben INEC

Kungiyar gamayyar jam'iyyun Najeriya 60 ta yi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben 2019, Atiku Abubakar da ya hakura da maganar neman duba rumbun tattara sakamakon zaben INEC.



Kungiyar a taron manema labarai data shirya wanda Alhaji Mohmmed Shittu yayi magana da yawunta ta bayyana cewa, suna rokon Atiku daya hakura da maganar leka rumbun tattara sakamakon zaben INEC, hakan be kamata ba.

Tace  tun kamin zabe INEC ta zauna da jam'iyyun siyasar kasarnan kuma sun bata abubuwan da suke so ta yi wanda babu maganar amfani da rumbun tattara sakamako kuma ta yi abinda zata iya daidai gwargwado dan haka basu ga dalilin da zai sa wata jam'iyya ta ware tace ita sai an nuna mata rumbun tattara sakamakon zabe ba.




Kungiyar ta kara da cewa, tana kuma kalubalantar yanda kungiyar masu sa ido ta turai tace wai ba'a yi ingantaccen zabe ba, tace shin wai ba 'yan Najeriya bane suka san ko an yi zabe me inganci ba ko kuwa a'a?

A karshe, kungiyar ta yi kira ga shugaba Buhari da yayi kokarin sakawa dokar zaben da majalisa ta mika mai Hannu.

A baya dai hutudole.com ya ruwaito muku labarin yanda Atiku da PDP zasu daukaka karar neman a basu damar leka rumbun tattara sakamakon zaben INEC  inda sukace basu yadda da hukuncin da kotun sauraren zabe ta yanke ba.

No comments:

Post a Comment