Pages

Wednesday 26 June 2019

David Silva zai bar Manchester City

Dan wasan tsakiya na Manchester City David Silva ya ce zai bar kulob din bayan shafe shekara 10 a karshen kakar 2019-20.


Dan kwallon na kasar Sifaniya, mai shekara 33, ya lashe kofin Firimiya hudu, FA biyu da kuma kofin League hudu tun bayan da ya koma kulob din a 2010, inda ya buga wasa 395.

Ya taka leda sau 33 a gasar Firimiyar da ta gabata inda ya zura kwallo shida domin taimakwa tawagar ta Pep Guardiola sake lashe kofin a karo na biyu a jere.


An tambaye shi ko zai zauna a kungiyar bayan kaka mai zuwa sai ya ce: "A'a, wannan ce shekara ta ta karshe."

Ya kara da cewa: "Shekara goma sun isa, wannan ne lokacin da ya fi dacewa da ni.

"Da farko City sun bukaci na sake sa hannu kan yarjejeniyar shekara biyu, amma sai na yanke shawarar sanya daya domin na yi ritaya bayan shekara 10.

"Hakan ne cikamaki. Komai zai kammala. Ba zai yiwu na koma wani kulob din da zai fafata da City ba. Don haka shekara 10 ta isa."
BBChausa.


No comments:

Post a Comment