Pages

Wednesday 26 June 2019

Yadda Daliban Sakandire Ke Rubuta Jarrabawar Karshe A Kasa

Wannan wata makarantar jeka ka dawo ce dake a cikin birnin Katsina, a K'ofar 'Yandaka.


Daliban makarantar ne ke rubutun jarabawar kammala sakandire wato SSCE, inda za ka ga wasu gasu nan a k'asa wasu kuwa a tsaye.

Ita dai wannan makaranta, galibi 'yay'an talakkawa ne ke zuwa domin neman Ilmi.



Idan har makarantar dake a birni ta samu kanta a wannan hali, ina ga makarantun kauyika ya za su kasance? 

Babu shakka wannan manuniyace dake nuna yadda ilmi ya samu tawaya a jihar Katsina da ma kasar baki daya. 

Ya kamata gwamna Aminu Bello Masari ya zage damtse kwarai da gaske domin ganin ya kawo gyara a wannan fanni da ma sauran fannoni masu matsala irin haka.






No comments:

Post a Comment