Pages

Tuesday 25 June 2019

Kasar Amurka ta samu tabin Hankali>>Inji Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya mayar da martani dangane da takunkumin da Amurka ta sanya wa Jagoran addinin Iran din, Ayatollah Khamenei.


Rouhani ya kara bayyana takunkumin da aka sanya wa Ayatollah Khamne'i da kuma wanda aka yi barazanar kakaba wa ministan kasashen waje na Iran din da "zancen banza".

Har wa yau, Shugaban na Iran ya kuma bayyana Fadar White House da 'sokwaye'.

Shugaba Donald Trump ya ce zai kakaba wa kasar Iran takunkumi mai tsauri wanda zai shafi shugaban addini Ayatollah Khamenei kai-tsaye.

Mista Trump ya ce ya dauki matakin ne bisa harbo jirgin sama kasar mara matuki da Iran din ta yi da kuma "laifuka da yawa".



"An kebance Ayatollah Khamenei ne saboda shi ne ke da alhakin duk abin da gwamnatin Iran take aikatawa," in ji Trump.

Rashin jituwa tsakanin kasashen biyu yana kara tabarbarewa a 'yan kwanakin nan.

Sakataren baitil malin Amurka Steve Mnuchin ya ce wannan takunkumin zai shifi biliyoyin daloli na kadarorin Iran, wanda dama can ya fara aiki tun kafin ta harbo jirgin na Amurka a yankin Gulf a makon da ya gabata.

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya ce shugaban Trump "ba ya la'akari da tsarin diflomasiyya kuma burinsa kawai shi ne a tafka yaki".
BBChausa.

No comments:

Post a Comment