Pages

Tuesday 25 June 2019

ZAMFARA: Kwamitin Bincike ya ce Yari ya yi wa naira biliyan 250 hadiyar-lomar-tuwo

Kwamitin Karbar Mulki da Bincike wanda Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kafa, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari ya yi wa naira biliyan 250.9 hadiyar-lonar-tuwo.


Hakan ya fito fili ne jiya Litinin a lokacin da Shugaban Kwamitin, kuma tsohon Mataimakin Gwamna na Yari, Ibrahim Wakkala ya mika rahoton binciken shi.

Wakkala ya ce: “Kwamiti na a lokacin da ta tantance yawan basussuka da tabargazar da gwamnatin da ta sauka kwanan nan ta tafka a karashin Abdul’aziz Yari, ta bi ta karbi rahoton da shi Yari din ya kafa masu binciken sa suka gudanar kafin saukar sa.


“Mun bi wannan hanya, mun dawo mun sake bin wata mu na nema, amma mun rasa inda zunzurutun kudade har naira biliyan 250 suka shige.


“Daga cikin wadannan kudade kuwa har da tulin bashin naira biliyan 115,190,477,572.00 wadanda ba a kai ga biyan masu ayyukan kwangilolin da aka rubuta ana gudanarwa ba har 462.

“Akwai kuma kudin garatutin ma’aikata har naira biliyan 1,431,645,305.99

“Sannan kuma Hukumomin Shirya Jarabawa na bin Jihar Zamfara basussukan NECO da na WAEC har naira biliyan 2.8” Inji Wakkala.

Ya kara da cewa gwamnatin Yari ta fitar da naira biliyan 2 da nufin biyan garatutin ma’aikata, amma an gano cewa naira miliyan 400 kadai ta biya ga Manyan Sakatarorin da suka yi ritaya kawai.

An rasa yadda aka yi sa sauran cikon naira bilyan 1.6, kamar yadda rahoton Wakkala ya wallafa.

Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na Yari, Ibrahim Dosara, ya ce duk babu gaskiya a cikin bayanan kwamitin.

“Karairayi ne kawai, amma ka jira na dawo daga Umra zan ba ka cikakken bayanin komai dalla-dalla.”

Haka Dosara ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES ta wayar tarho.


No comments:

Post a Comment