Pages

Sunday 23 June 2019

Tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya na so kasar Amurka da Iran su gwabza yaki: Saboda Najeriya zata amfana>>Injishi

Matashin dan takarar shugaban kasa a babban zaben daya gabata, Adamu  Garba II ya bayyana cewa shi fa a ra'ayinshi yana son kasashen Amurka da Iran su gwabza yaki dan kuwa yana ganin Najeriya zata amfana da hakan.



A sakon daya rubuta ta shafinshi na dandalin Twitter, Garba yace, Fadan Amerika da Iran zai sa farashin danyen mai ya tashi sosai wanda kuma hakan zai taimakawa Najeriya sosai wajan samun kudin shiga dan haka shi yana ganin yin yakin shi yafi dacewa.

Saidai ya samu martani da dama inda wasu suka goyi bayanshi,wasu kuwa sukace sam wannan ba tunani me kyau bane.

Daya daga cikin wanda suka soki wannan ra'ayi na Garba ya bayyana cewa, kai garama da Allah yasa ka janye daga takarar shugabancin Najeriya, zabenka ka zama shugaba  mutane miliyan 200 ka iya zama wani babban bala'i.

Ta yaya zaka goyi bayan a yi yaki kawai dan cimma wata manufa taka.

Sai Garba ya bashi amsar cewa, idan fahimtarka da amfanin da 'yan Najeriya zasu samu daga wannan yaki shine abin amfanuwata, to lallai dole in godemaka dan ka yabenine. Abinda ya kamata kawai mu mayar da hankali akai shine ci gaban kasar mu. Babu abinda ya shafeka da rayuwar mutanen kasashen Iran ko Amerika, 'yan Najeriya ya kamata ka damu dasu.

Bayan da shugaba kasar Amurka ya janye kaiwa Iran harin ramuwar gayya na soji, Garba ya bayyana cewa to shikenan tunda ita amurkar ta kasa, kamata yayi ita Iran din ta fara kai hari, saboda lura da cewa akwai sarakunan kasar da suka gabata da basu taba yin rashin nasara a yaki ba.

No comments:

Post a Comment