Pages

Thursday 18 July 2019

AFCON: Najeriya ta yi na uku bayan doke Tunisia

Odion Ighalo ne ya zura kwallo daya tilon da ta bai wa Najeriya damar doke Tunisia a wasan neman na uku na gasar cin kofin kasashen Afirka.


Ighalo, wanda shi ne ya fi kowa cin kwallo a gasar bayan da ya zura biyar, ya ci kwallon ne bayan da golan Tunisia Moez Ben Cherifia ya kawar da kwallo daga hanyar dan wasansu na baya Yassine Meriah.

A wasan da duka bangarorin biyu ba su nuna kuzari sosai ba, Tunisia ta kai hari ta hannun Ferjani Sassi da Ghaylene Chaalali.


Najeriya kuma ta kai munanan hare-hare ta hannun Samuel Chukwueze da Samuel Kalu.

Sau takwas kenan Najeriya, wacce sau uku tana lashe kofin, tana zama ta uku a gasar.

Senegal za ta yi fatan lashe kofin a karon farko a tarihinta a wasan karshen da za ta fafata da zakarun 1990, Aljeriya, a ranar Juma'a.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment