Pages

Thursday 22 August 2019

Abin da ya sa muka kara yawan ministoci>> Buhari

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce sun kara yawan ministoci ne "saboda arzikin kasar ya karu".

Mai magana da yawun fadar shugaban Garba Shehu ne ya fadi haka a wata hira ta musamman da BBC jim kadan bayan kammala bikin rantsuwar.

Shugaba Buhari ya rantsar da ministoci 43 a ranar Laraba sabanin 36 da ya bai wa mukamai a karon farko na gwamnatinsa.




Har wa yau, Shugaba Buhari ya kirkiro wasu sababbin ma'aikatu guda biyu, wadanda su ma suka samu dacewa da nasu ministan.

Ma'aikatun sun hada da: Ma'aikatar Jin-kai da Walwalar 'Yan kasa wato Ministry of Human Affairs, Disaster Mangagement and Social Development, wacce Sadiya Umar farouk za ta jagoranta, sai kuma Ma'aikatar Harkokin 'Yan Sanda wato Ministry of Police Affairs, wacce Mohammed Maigari Dangadi zai jagoranta.

Garba Shehu ya ce a karon farko Shugaba Buhari ya rage ministocin ne saboda su dace da aljihun gwamnati.

Wakilinmu Ishaq khalid ya tambaye shi ko ina makomar matse bakin aljihu da tsimi na wannan gwamnati ya kwana?

"Ai ba a fasa wannan ba, tsumin tattalin arziki yanzu aka fara shi domin kuwa wannan taro da aka yi da su ministocin an fada cewa akwai mataki na zabge kudaden tafiyar da gwamnati da za a dauka.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment