Pages

Wednesday 21 August 2019

Sabbin ma'aikatun da shugaba Buhari ya kirkiro

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya rantsar tare da baiwa sabbin ministocinshi ma'aikatun da zasu yi aiki a karkashi a yau, Laraba, saidai akwai sabbin ma'aikatu da shugaban ya kirkiro wanda babu su a zangon mulkinshi na farko.




Wadabnan ma'aikaru sune:

Ma'aikatar wutar lantarki wadda a baya take karkashin Babaraji Fashola a yanzu Injiniya Sale mamman ne ministan Ma'aikatar.

Ma'iakatar Ayyuka na musamman da lamurran da suka shafi alaka tsakanin gwamnatoci, George Akume ne ministan wannan ma'aikata.

Ma'ikatar kula da lamurran jama'a, dana ibtila'i da Bunkasa rayuwar Talakawa, Sa'adiya Umar Faruk ce ministar wannan ma'aikata.

Ma'aikatar 'yansanda wanda Muhammad Maigari Dingyadine ministan wannan ma'aikata.

Sai kuma ma'aikatar kula da sufurin jiragen sama wadda a baya take karkashin Rotimi Amaechi a yanzu kuma tana zaman kantane a karkashin ikin Hadi Sirika.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment