Pages

Wednesday 21 August 2019

EFCC ta yi wa gidan tsohon Gwamnan Lagos dirar mikiya

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC ta kai samame gidan tsohon Gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode, a wani bangare na ci gaba da binciken da ake yi masa kan ruf da ciki da dukiyar gwamnati.




Mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade ya tabbatar wa manema labarai cewa, Ambode wanda bai dade da sauka daga karaga ba, na fuskantar tuhuma kan cin hanci fa rashawa.

Da misalin karfe 9:35 na safiyar wannan Talatar agogon kasar ne, EFCC ta kai samamen a gidansa da ke Epe a jihar Lagos.

Ana zargin tsohon Gwamnan da bartanar da biliyoyin Naira a tsawon shekaru hudu da ya kwashe yana mulki a jihar, yayinda aka dakatar da asusunsa na banki dauke da makudaden kudade makwanni biyu da suka gabata.
RFIhausa.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment