Pages

Wednesday 21 August 2019

Rikicin Boko Haram zai iya kaiwa nan da shekaru 15 kamin a yi magananinshi>>Obasanjo


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwa kan yawan al'ummar Najeriya inda yace bincike ya nuna nan da shekaru 30 yawan Al'ummar Najeriya zai kai miliyan 450.

Ya kara da cewa yawan yaran dake gararamba akan titi basa zuwa makaranta ne ke taimakawa ayyukan ta'addanci da ake fama dasu cikin kasarnan.

Yayi wannan maganane a wajan wani taron kungiyar matasa dake karkashin dakin karatunshi dake cikin gonarshi a Abekuta a kokarin ganin ci gaban matasan.

Ya kara da cewa muddin gwamnati bata yi wani abu ba kan kula da yaran da basa zuwa makaranta ba to fadan Boko Haram zai iya kai nan da shekaru 15 kamin  a yi maganainshi

"Be kamata a samu wani yaro a Najeriya da bai zuwa makaranta ba"

"Idan kuma ba a dauki matakin daya dace ba akan hakan to nan da shekaru 15 Boko Haram zata ci gaba da wanzuwa".inji shi.

Obasanjo ya bayar da labarin yanda shi da marigayi janar Murtala suka canja akalar najeriya bayan yakin basasa na 1970 inda ya baiwa matasan kwarin gwiwar cewa Najeriya zata gyaru.

"Na yi mulkin Najeriya a lokacin da da dama suka karaya da cewa Najeriya ba zata gyaru ba amma amma mun dawo da ita bisa turba"

Ya ci gaba da cewa "Na yadda da Najeriya kuma na yadda cewa zata gyaru"

"A lokacin mulkin Murtala Muhammad da mulkina sojojin dake aiki a Legas dake amfani da motocin haya dan zuwa gurin aiki basa iya saka kakinsu saboda kunya amma a cikin watanni 6 abubuwa suka canja, sojojin suka fara saka kayansu sun alfahari da kansu, to ina gaya muku Najeriya zata ci gaba" injishi.

"Kada ku sare, duka da cewa Najeriya na cikin matsanancin hali a yanzu, komai zai wuce kuma zata gyaru" inji Obasanjo.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment