Pages

Wednesday 21 August 2019

Sabbin hotunan dukan da inyamurai sukawa Sanata Ekweremadu a kasar Jamus sun nuna cewa a gaban 'yansandan kasar abin ya faru


Wasu sabbin hotuna da suka bayyana kan jibgar da Inyamurai masu fafutukar kafa kasar Biafra da akewa lakabi da Ipob suka wa tsohon mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Ike Ekweremadu a kasar Jamus ya bayyana. Banbancin wadannan hotunan da na baya shine ashe a gaban jami'an tsaron kasar ne Ekweremadu ya sha duka ba tare da sun tabuka komai ba.



Ekweremadu dai da inyamuran suka rufashi da jifa da dutse da kwai tare da yaga riga da cire hula ya kuma ga basu da niyyar kyaleshi haka sai ya ranta a na kare ya falla da gudu dan tsira da rayuwarshi.






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment