Pages

Thursday 22 August 2019

SANATAN KADUNA: Kotu Ta Kori Karar Shehu Sani

Kotun dake sauraron karar zabe ta Majalisar Wakilai dana jiha ta yi fatali da takardar koken da tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin inuwar jamiyyar PRP Shehu Sani ya shigar na kalubalantar abokin takarar sa Sanata Uba Sani wanda a yanzu shine zaɓaɓɓen dan Majalisar Dattawa dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a a inuwar jamiyyar sa ta APC.


Alkalin Kotun mai Shari’a  A. H. Sulaiman bayan da ya shafe awanni biyu yana yanke hukuncin, ya dauki matakin yin watsi da ƙarar ta Shehu Sani ce saboda rashin kwararan hujjoji a kan karar da ya shigar a gaban Kotun.

Mai Shari’ a A. H. Sulaiman ya sanar da cewa, Kotun ta yanke wannan hukuncin a bisa hujjojin da aka  gabatar a gabanta.

Lauyan dake jagorantar karar ta Sanata Uba Sani, Barista Frank Ikpe, yace Kotun ta tabbarwa da   Sanata Uba Sani zaben sa da akayi a bisa kwararan hujjojin da aka gabatar mata.

Shima dayan  lauyan dake cikin tawagar lauyoyin Sanata Uba Sani,   Sulaiman Shu’aibu ya sanar da cewa hukuncin da Kotun ta yanke ya yi daidai, inda kuma ya shawarci wadanda suke da ja da hukuncin Kotun, suna iya daukaka qara idan basu gamsu ba.

A nashi martanin a kan hukuncin Kotun daya daga cikin tawagar Lauyoyin dake kare Sanata   Uba Sani Barista Abdulra’uf Atiku ya jinjinawa Kotun a kan hukuncin data yanke, inda yace, Kotun ta yi adalci a yanke hukuncin.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment