Pages

Thursday 22 August 2019

Saudiyya ta ba matan kasar 'yancin tafiya ba tare da izinin mazan da ke kula da su ba

A karon farko gwamnatin Saudiyya ta samar da dokar da ta ba wa matan kasar yin tafiya zuwa kasashen waje ba tare da izinin wani waliyyinsu ba.


Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya rawaito wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida na cewar an ba wa ofisoshin kula da fasfo da aure umarnin aiwatar da wannan doka.

Jami'in ya ce duk masu son karin bayani game da wannan tsari su tuntumi hukumomin da abun ya shafa.

A ranar 2 ga watan Agusta ne Saudiyya ta fitar da wani kudirin doka da ya ba wa matan kasar damar yin fasfo da tafiya zuwa kasashen waje ba tare da izinin miji, uba ko dan uwa na jini ba.

A baya dai a Saudiyya mata da maza 'yan kasa da shekaru 21 ba sa iya fita zuwa kasashen waje ba tare da izinin waliyyai ko mazajensu ba.

Haka zalika an janye dokatar da ta wajabta dole ne adireshin mace ya zama na inda mijinta ko iyayenta suke.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment