Pages

Friday 23 August 2019

Tsohon dan wasan Ghana ya mutu

Tsohon dan wasan Ghana wanda ya taka leda a Nottingham Forest da Bristol Rovers, wato Junior Agogo ya yi ban kwana da duniya yana da shekaru 40.




A shekarar 2015, Agogo ya gamu da cutar shanyewar barin jiki, rashin lafiyar da ta kai shi ga fuskantar kalubalen furta magana.

Tuni tsoffin kungiyoyin da ya taka leda suka mika sakwanin ta’aziyar rasuwarsa.

Agogo wanda ya fara taka leda a Sheffield, ya buga wa kasarsa ta Ghana wasanni 27, yayinda ya ci mata kwallaye 12.

Magoya bayansa za su ci gaba da tuna shi musamman kan kwallaye ukun da ya zura a ragar Najeriya a wasan da kasashen biyu suka buga a Gasar Cin Kofin Kasshen Afrika a shekarar 2008 a birnin Accra, abinda ya bai wa Ghana nasara a wancan lokaci.
RFIhausa.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment