Pages

Thursday 22 August 2019

'Yan Bindiga Sun Shigo Har Gida Sun Sace Wani Dan Majalisa A Jihar Sokoto

"Jama'a muna barar addu'a gare ku. Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da mai gidan mu, kuma dan majalisar dokoki mai wakiltar Dange Shuni a majalisar dokoki ta jihar Sakkwato, Hon. Alh. Aminu Magaji Bodai, a gidan sa dake cikin mahaifar sa ta Bodai  a daren jiya Laraba misalin karfe 12:00.", cewar makusantan dan majalisar.


A 'yan kwankkin nan lamarin tsaro a jihar yana kara tabarbarewa, duk da kokarin sasantawa da gwamnatin jihar ke cikin yi da 'yan bindigar, domin a satin da ya gabata an bada sanarwar dawowar sace sace mutane a babbar hanyar Sokoto zuwa Zamfara. 

Sai dai wasu masu sharhi lamurran yau da kullum na cewa sabbin mukaman da jihar Sokoto ta samu a fannin tsaro na sabon ministan kula da lamurran 'yan sanda, Shugaban kwamitin tsaro, kwamitin SSS, kwamishinan 'yan sandar zamfara dan asalin jihar Sokoto ne, ana ganin idan wadannan shugabannin suka ajiye ra'ayin siyasa suka yi aiki tare da gwamnatin jihar da Sarakuna, to lalle za'a samu gagarumin nasara, idan ko suka kasa hada kan su saboda bambancin siyasa, to labarin ba zai haifar da da mai ido ba.
Rariya.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment