Pages

Thursday 22 August 2019

'Yan garin gawurtaccen me satar mutanen da yayi sanadiyyar kisan sojoji sun bayyana rashin jin dadin kamashi: Ya bayyana yanda yake biyan sojoji cin hanci


media
A yayin da 'yan Najeriya da dama ke murnar kama gawurtaccen jagoran masu satar mutane dan neman kudin fansa da yayi sanadiyyar kisan wasu jami'an 'yansanda, Watau Hamisu Bala Wadume, su kuwa mutanen garinsu bakin ciki suke da kamun nashi inda sukace mutum ne me taimakon Al'umma.



Mutanen garin Ibi, mahaifar Wadume sun bayyana cewa labarin kamunshi abin bakin cikine dan kuwa mutum ne me taimako, kamar yanda wani Yahaya me kifi ya bayyana.

"Mutum ne me taimako kuma baya nuna banbancin addini ko kabila", Yahaya ya gayawa Punch.

Maikifi ya ci gaba da cewa"Yanzu haka akwai masallacin da Wadume ke ginawa a garin kuma an kusa kammalashi amma kamun da aka mai zai tsayar da aikin gina masallacin"


Wani mazaunin Ibi me suna Micheal Adi ya bayyana cewa ranar da sanarwa ta samesu cewa an kama Wadume duk sun shiga cikin wani yanayi.

"Maganar gaskiya ya taimaki mutane da yawa a garinnan inda wasu ma shine ya zama sanadin arzikinsu sannan rijiyar burtsatsen da yayi mana ba zamu tana mantawa dashi ba" inji Micheal

Saidai tsohon shugaban rukon kwarya na karamar hukumar Ibi, Adasho Johnson ya bayyana cewa sun ji dadin kama Wadume domin kuwa hakan zai sa su samu saukin mamayar da jami'an tsaro suka wa garin nasu suke kama mutane sanadiyyar tserewarshi.


Ya kara da cewa abinda zasu jira su gani shine bincike da zai tabbatar da ko Wadume na da laifi ko kuwa akasin haka.

Wani sabon rahoto daga The Nation kuma na cewa a ci gaba da binciken da 'yansanda kewa Wadume ya bayyana musu cewa yana biyan sojojin dake kan hanya dubu 20 dan su barshi ya wuce.

Ya kuma kara da cewa sati 3 da suka gabata ya aika wa da jami'in sojan daya taimaka mishi ya tsere watau Kyaptin Tijjani Balarabe da makudan kudi ta asusun ajiyar kudinshi na banki.

Wata majiyar 'yansanda da ta tsegumtawa The Nation labarin tace a ranar da aka kama Wadume, wasu yaran Kyaftin Balarabe sun kirashi suka gayamai cewa an kama mutuminshi, nan Kyaptin Balarabe ya basu umarnin zuwa su kwatoshi.

Inda bayan sun kwatoshi suka kaishi gidan Kyaptin Balarabe aka kira me walda ya yanke ankwar da aka daura mai a hannu.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment