Pages

Thursday 22 August 2019

Yanda Messi ya taimakamin na zama gwanin dan kwallo>>Ronaldo


Lionel Messi,Cristiano Ronaldo
Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya bayyana yanda takarar da suke yi da Messi tasa ya kara zama jajirtacce wajan ganin yayi abinda ya kamata dan samun nasarori.



Ronaldo da Messi sun kasance abokan gasa tsakaninsu na kusan shekaru 9 lokacin Ronaldon na Kungiyar Real Madrid inda suka jera shekaru 10 suna lashe kyautar gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or tsakaninsu.

A yayin hira da wata kafar watsa labarai ta kasar Portugal me suna TVI, Ronaldo ya bayyana cewa, Tabbas Messi yasa na zama tauraron dan kwallo hakanan nima nasa ya zama tauraro, idan na lashe wata gasa to abin yana zama kalubale a gareshi kamar na tsikareshine dan ya kara himma hakanan nima idan ya lashe wata gasa ina samun karin karfin gwiwar dagewa in yi kwallo da kyau.

Irin kwallon da yake bugawa tana birgeni hakanan shima a baya ya bayyana rashin jin dadinshi dana bar Real Madrid saboda yana jin dadin gasar da muke tsakaninmu, injishi

"Amma irin gasar da muke me tsafta ce" Ronaldo ya karkare.



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment